A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, littafin Muhawara 101 Masu Ban Sha’awa da Karantawa, wanda Muhammad Muhammadi Ishtihardi ya rubuta, ya tattara muhawarori daban-daban da suka shafi batutuwan aƙida da addini. Kamfanin Dillancin Labaran Hauza zai riƙa wallafa wasu daga cikin waɗannan muhawarori a cikin lokuta daban-daban.
Annabi (SAWA) Ya Yi Busharar Cewa Tawagar Zalunci (Fi'atul Baghiya) Za Su Kashe Ammar
Ammar Ibn Yasir yana ɗaya daga cikin manyan sahabban Manzon Allah (SAWA). Bayan wafatin Annabi (SAWA), ya ci gaba da bin tafarkin Musulunci na gaskiya da kuma biyayya ga Imam Ali (AS), har ya yi shahada a Yaƙin Siffin.
Manzon Allah (SAW) ya taɓa gaya masa cewa:
«تَقْتُلُکَ الْفِئَةُ الْبَاغِیَةُ»
Ma’ana: “Tawagar azzalumai ce za ta kashe ka.”
Musulmi da dama sun ji wannan magana, kuma ta shahara a tsakaninsu cewa Manzon Allah (SAWA) ya faɗi hakan ne game da Ammar.
Shekaru suka shuɗe, har aka shiga zamanin halifancin Imam Ali (AS), inda yaƙi ya ɓarke tsakanin rundunarsa da rundunar Mu’awiya. An san wannan yaƙi da Yaƙin Siffin. Ammar Bin Yasir yana cikin rundunar Imam Ali (AS), kuma bayan ya nuna jarumta da sadaukarwa sosai, sojojin Mu’awiya suka kashe shi.
Waɗanda suke cikin shakku game da wane ne yake kan gaskiya tsakanin Mu’awiya da Imam Ali (AS), daga wannan lamari cewa, sun fahimci cewa bisa ga maganar Manzon Allah (SAWA), rundunar Mu’awiya ce tawagar zalunci, domin ita ce ta kashe Ammar Yasir. Saboda haka, suka fahimci cewa Mu’awiya yana kan ɓata.
Mu’awiya Ya Yi Iƙirarin Cewa Imam Ali (AS) Ne Ya Kashe Ammar
A wannan lokaci, Mu’awiya ya ga cewa mutuwar Ammar Bin Yasir tana raunana ruhin rundunarsa, kuma tana iya haifar da rarrabuwar kai a cikinta. Nan take ya yi amfani da wata magana ta yaudara, yana mai cewa: “Imam Ali (AS) ne ya kashe Ammar Bin Yasir, ba ni ba. Domin da Imam Ali bai tura shi yaƙi da ni ba, da ba a kashe shi ba!”
Wannan magana ta Mu’awiya ta ruɗi wasu daga cikin Musulmi.
Amsar Imam Ali (AS) Ga Mu’awiya
A lokacin da Imam Ali (AS) ya ji wannan karkatacciyar hujja, nan take ya ba da amsa, yana cewa: “Idan maganar Mu’awiya ta kasance daidai, to ya kamata mu ce Manzon Allah (SAWA) ne ya kashe Hamza (AS), wanda mushrikai suka kashe a Yaƙin Uhudu, domin shi ne ya tura shi yaƙi!”
Abdullahi, ɗan Amr bin As, ya kai wannan amsa ga Mu’awiya. A cewar labarin, Mu’awiya ya fusata ƙwarai, har ya ce wa Amr bin As, mashawarcinsa mai amfani da dabarun yaudara: “Ka fitar da ɗanka wawa daga wannan majalisar!”
Manazarta:
1. A’yanush Shi’a, juzu’i na 42, shafi na 215.
Ra'ayinka